Sabon Shugaban Zimbabwe Ya Rusa Majalisar Ministocin Tsohon Shugaba Mugabe
(last modified Tue, 28 Nov 2017 05:18:55 GMT )
Nov 28, 2017 05:18 UTC
  • Sabon Shugaban Zimbabwe Ya Rusa Majalisar Ministocin Tsohon Shugaba Mugabe

Sabon shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya rusa majalisar ministocin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe a wani abin da ake gani a matsayin matakin farko na tabbatar da ikonsa a kasar.

Gidan talabijin din ZBC mallakar gwamnatin kasar ne ya sanar da hakan a jiya Litinin cikin wata sanarwa da sabuwar gwamnatin ta fitar inda ta ce lokaci yayi da za a kafa sabuwar gwamnati don tabbatar da ci gaban kasar. Sanarwar ta kara da cewa shugaban kasar ya bar ministoci biyu da suka fito daga tsohuwar gwamnatin a matsayinsu na ministoci; su ne kwa Patrick Chinamasa a matsayin ministan kudi sai kuma Simbarashe Mumbengegwi a matsayin ministan harkokin waje.

Sanarwar ta kara da cewa a yau Talata din nan shugaba Mnangagwa zai gana da manyan daraktocin dukkanin ma'aikatun gwamnatin kasar don tattaunawa da su kan yanayin kasar wanda ake ganin hakan a matsayin wani share fage ne na kafa sabuwar gwamnatin da shugaban yake son yi.

A ranar Juma'ar da ta gabata ce shugaba Mnangagwan ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar, kwanaki uku bayan da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya sanar da murabus dinsa daga shugabancin kasar sakamakon matsin lambar da ya fuskantar don bayan kwace madafun iko da sojojin kasar suka yi bayan kimanin shekaru 37 yana mulkin kasar.