Gambiya: An Gabatar Da Sojoji 10 Bisa Zargin Kitsawa Gwamnati Makarkashiya
(last modified Tue, 28 Nov 2017 12:12:44 GMT )
Nov 28, 2017 12:12 UTC
  • Gambiya: An Gabatar Da Sojoji 10 Bisa Zargin Kitsawa Gwamnati Makarkashiya

Kamfanin dillancin labarun faransa ya nakalto cewa an gabatar da sojojin ne a jiya litinin bisa tuhumar laufukan bijirewa aiki da umarni da kuma kitsa makarkashiyar kifar da gwamnati a watan Yuni.

Baya ga sojojin 10, an kuma gurfanar da wasu 2 da su kuma aka tuhuma da take doka da kuma taimakawa  wasu da ake tuhuma da guduwa.

Har ila yau wasu sojojin suna fuskantar tuhuma akan ci gaba da nuna biyayya ga tsohon shugaban kasar Yahya Jameh wanda ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 22.

Ana yi wa sojojin da aka kama shari'a ne a cikin kotun soja.