An Bude Taron Koli Na Turai Da Afrika
Nov 29, 2017 17:12 UTC
An bude taron shugabannin kasashen Turai da na Afrika karo na biyar a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast a yau Laraba.
Shuwagabanni kasashe dana gwamnatoci 83 ne da mahalarta 5,000 daga kasashe 55 na Afrika da na turai 28 ne ke halartar taron.
Taron na wannan karo da aka ma taken zuba jari don taimakawa matasa, na kuma maida hankali kan kwararar bakin haure 'yan Afrika zuwa Turai da kuma ta'addanci.
Babban batun da ake sa ran shugabannin kasashe da dama musamen daga Afrika zasu tabo, shi ne labarin cinikin bakin haure tamakar bayi a kasar Libiya.
Daga cikin shuwagabannin dake halartar taron harda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaba Emanuelle Macron na Faransa.
Tags