An Hallaka Mayakan Ashabab A Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25935-an_hallaka_mayakan_ashabab_a_somaliya
Dakarun kasar Somaliya sun hallaka mayakan ashabab 11 a tsakiyar kasar
(last modified 2018-08-22T11:31:04+00:00 )
Dec 01, 2017 18:07 UTC
  • An Hallaka Mayakan Ashabab A Somaliya

Dakarun kasar Somaliya sun hallaka mayakan ashabab 11 a tsakiyar kasar

kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya habarta cewa a wannan juma'a an tabka kazamin fada tsakanin dakarun kasar somaliya da mayakan 'yan ta'addar Ashabab a kauyen Hiran dake tsakiyar kasar, lamarin da yayi sanadiyar hallakar mayakar 'yan ta'addar 11 da kuma mutuwar soja guda tare da jikkatar wasu 4 na daban.

Babban komandan sojojin yankin Hiran ya ce fadan ya fara ne a yayin da mayakan 'yan ta'addar ashabab din suka kaiwa tawagar gwamnatin yankin hari. 

Tuni dai kungiyar ta ashabab ta dauki alhakin kai harin, inda ta ce ta hallaka sojojin gwamnati guda uku tare da kona wata mota ta gidan gwamna guda.

Wata majiya mai zaman kanta a yankin ta ce harin yayi sanadiyar jikkatar sojojin kasar11, kungiyar Ashabab dai ta yi alkawarin ci gaba da yakar gwamnatin somaliya, inda a cikin 'yan kwanakin nan ta zafafa kai hare-harenta a kan manbobin gwamnatin kasar.