Somaliya: An Kashe 'Yan Kungiyar al-Shabab 11
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25945-somaliya_an_kashe_'yan_kungiyar_al_shabab_11
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ce an yi fada a tsakanin sojojin gwamnatin kasar ta Somaliya tare da 'yan kungiyar ta al-shaba, da ya kai ga kashe 'yan ta'addar 11.
(last modified 2018-08-22T11:31:05+00:00 )
Dec 02, 2017 07:24 UTC
  • Somaliya: An Kashe 'Yan Kungiyar al-Shabab 11

Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ce an yi fada a tsakanin sojojin gwamnatin kasar ta Somaliya tare da 'yan kungiyar ta al-shaba, da ya kai ga kashe 'yan ta'addar 11.

Majiyar sojan kasar ta ce fada ya barke ne a tsakanin bangarorin biyu bayan da mayakan al-shabab suka kai wa ayarin gwamnati hari.

Tun da fari, mayakan na al-shabab sun dauki alhakin kai wa gwamnan yankin hari tare da kashe sojoji uku da kuma kona motar soja guda.

Wata majiya mai zaman kanta  ta ce sojojin gwamnati 11 suka rasa rayukansu.

Kungiyar al-shabab tana a matsayin kalubale ta fuskar tsaro ga gwamnatin Somaliya da kuma kasashen makwabta.