Sudan ta yi barazanar rufe iyakarta da kasar Sudan ta kudu.
Magabatan Khartum sun zarki kasar Sudan da taimakawa kungiyoyin 'yan tawayen kasar tare da yin barazanar rufe iyakarsu.
A wata sanarwa da ya fitar jiya Alkhamis, Ibrahim Mahmud mashawarcin shugaban kasar sudan ya bayyana cewa idan har magabata birnin Juba ba su kawo karshen taimakon da suke baiwa 'yan tawayen kasar ba, Khartum ba ta da wani zabi face ta sake rube iyakokin kasar daga kudu.
Magabatan birnin Khartum na zargin takwarorinsu na Juba da taimakawa 'yan tawayen yankin Darfur da suke naman ballewar jahohin Kirdufan da Nil Aby.
A shekarar 2011 sudan ta kudu ta balle daga kasar Sudan, daga kuma wannan lokacin zuwa yanzu an sha rufe iyakokin kasashen biyu, bayan sasantawa a sake bude su.
A jiya Alkhamis, Kafafen watsa labaran kasar Sudan sun habarta cewa, Gwamnati ta dauki wani mataki na takurawa Al'ummar kasar Sudan ta kudu mazauna kasar ba a kan ka'ida ba. ya zuwa yanzu dai Al'umma na dora ayar tambaya kan dalilin da ya sanya magabatan khartum din suka dauki wannan mataki a yayin da ake shirye- shiryan gudanar da taron sulhu tsakanin Gwamnatin da kungiyoyin 'yan adawa gami da na 'yan tawaye gobe Assabar a birnin Adis Ababa fadar milkin kasar Ethiopia.