Zimbabwe : Mnangagwa Ya Yi Gajeren Garanbawul A Majalisar Ministocinsa
(last modified Sun, 03 Dec 2017 05:52:02 GMT )
Dec 03, 2017 05:52 UTC
  • Zimbabwe : Mnangagwa Ya Yi Gajeren Garanbawul A Majalisar Ministocinsa

Sabon shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya aiwatar da wasu sauye-sauye a majalisar ministocinsa, kwana biyu bayan ya sanar da kafa ta.

An yi sauye-sauyen ne saboda jerin sunayen da ya fitar daga farko ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya takaita adadin ministocin wadandan ba 'yan majalisar dokoki ba.

Daga cikin ministocin da aka sallama, har da na kwadago, Clever Nyathi, da kuma na ilimi Lazarus Dokora wanda dama ya ke shan suka kan rawar da ya taka wajen tabarbarewar harkar ilimi a kasar.

Lazarus Dokora an dai maye gurbinsa da Paul Mavima wata 'yar majalisar dokoki a karkashin jam'iyyar Zanu- PF mai mulki, inda shi ma  Clever Nyathi aka maye gurbinsa da wata yar majalisar ta jam'iyyar mai mulki, ko da ya ke an ba shi matsayi na mai bada shawara na musamen kan hadin kan kasa.