An Kashe Jami'an 'Yan Sanda 6 A Arewa Maso Gabashin Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26019-an_kashe_jami'an_'yan_sanda_6_a_arewa_maso_gabashin_najeriya
Hukumar 'yan sandar Najeriya ta snar da kashe jami'anta shida a wani rikicin manoma da makiya a garin Numan dake jihar Adamawa.
(last modified 2018-08-22T07:01:05+00:00 )
Dec 05, 2017 03:02 UTC
  • An Kashe Jami'an 'Yan Sanda 6 A Arewa Maso Gabashin Najeriya

Hukumar 'yan sandar Najeriya ta snar da kashe jami'anta shida a wani rikicin manoma da makiya a garin Numan dake jihar Adamawa.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto hukumomin 'yan sandar Najeriya na cewa wani rikici mai nasaba da kabilanci da kuma rikicin gonaki ya barke a kauyukan da ke kusa da garin Numan, lamarin da ya hana masu tafiya wucewa tare da tilasta wa wasu kauracewa daga garin Numan, kauyukan da aka kai wa hare-haren sun hada da Bono da Laworu da Dom, duka a kusa da garin Numan.

Usman Abubakar kakakin 'yan sandar jihar Adamawa ya bayyana cewa an tura jami'an 'yan sandar ne domin kwantar da tarzoma tare kuma da kwace makaman dake a hanun bangarorin biyu, sai rikcin ya ritsa da jami'an 'yan sandar guda shida.

Rahoton ya ce har yanzu babu wani mutum da aka kame a wannan rikici, a cikin 'yan kwanakin nan rikicin tsakanin manoma da makiya na kara tsananta, inda a ranar 20 ga watan Nuwambar da ya gabata, irin wni rikci ya lashe rayukan mutane 20 tare da jikkata wasu 30 na daban.