DRC : Zaman Dar-dar Sakamakon Yawaitar Girgiza Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26053-drc_zaman_dar_dar_sakamakon_yawaitar_girgiza_kasa
Rahotanni daga Jamhuriya Demukuradiyyar Kongo, na cewa ana cikin zaman dar-dar a yankinn kudancin Kivu, sakamakon samun girgiza kasa sau hudu tun daga farkon wannan wata.
(last modified 2018-08-22T07:01:06+00:00 )
Dec 05, 2017 14:14 UTC
  • DRC : Zaman Dar-dar Sakamakon Yawaitar Girgiza Kasa

Rahotanni daga Jamhuriya Demukuradiyyar Kongo, na cewa ana cikin zaman dar-dar a yankinn kudancin Kivu, sakamakon samun girgiza kasa sau hudu tun daga farkon wannan wata.

Bayanai daga kasar dai sun ce yankin Kudancin Kivu ya fuskanci girgiza a ranarkun Litini da yau Talata bayan an fuskanci hakan da ranar 1, zuwa 3 ga wannan watan Disamba da muke ciki lamarin da ya sanya fargaba a cikin zukatan mazauna yankin.

Tafkin Kifu wanda ya kai har zuwa tafkin Edouard har zuwa tafkin Tanganyika  ya kasance yankin mai girgiza a cewar Profesa Kacho Karume na hukumar sa ido kan tsaunuka masu tunbudin wuta na Goma (OVG). 

Karfin girgiza kasa da aka fuskanta a jiya Litini ya kai 4.5 a ma'unin Rishter, kuma ana fargabar karfibn zai iya kaiwa har zuwa 5 a cikin kwanaki masu zuwa kafin tafkin na KIvu ya daina bori.