Najeriya : Jonatan Ya Sake Bijirewa Sammacin Kotu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26057-najeriya_jonatan_ya_sake_bijirewa_sammacin_kotu
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebili Jonatan ya sake bijirewa sammacin babbar kotun Abuja kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon kakakin Jam’iyyar PDP mai adawa Olisa Metuh.
(last modified 2018-08-22T07:01:06+00:00 )
Dec 05, 2017 14:53 UTC
  • Najeriya : Jonatan Ya Sake Bijirewa Sammacin Kotu

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebili Jonatan ya sake bijirewa sammacin babbar kotun Abuja kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon kakakin Jam’iyyar PDP mai adawa Olisa Metuh.

Ana tuhumar Olisa Metuh ne da karbar naira miliyan 400 daga hannun tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki daga cikin kudaden da aka ware domin sayen makaman yaki da kungiyar Boko Haram.

Karo na uku kenan da Jonatan ke bijirewa sammacin kotun ta Abuja.

Metuh ya musanta zargin inda ya bukaci tsohon shugaban ya zama shaidarsa, amma duk kokarin mikawa tsohon shugaban sammacin kotu domin bada shaidar ta cutura.

Saidai wani wakilin Jonatan ya shaidawa alkalin kotun cewa, tsohon hsugaban zai halarci kotun a ranar Litini idan aka sake aike masa da wani sammaci.

Ana dai zargin an yi amfani da wani bangaren kudaden wajen yin yakin nemam zabewa tsohon shugaban Jonatan a 2015.