Kotu Ta Sake Dage Shari'ar Tsohon Ministan Kudin Zimbabwe Zuwa Gobe Alhamis
Wata kotu a kasar Zimbabwe ta dage sauraren shari'ar da a ke yi wa tsohon ministan kudin kasar Ignatius Chombo da ake zargi da rashawa da cin hanci zuwa gobe Alhamis don ci gaba da sauraren batun ba da belinsa da aka gabatar mata.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar alkalin kotun ya sanar da dage sauraren karar ne a yau din nan bayan da lauyan gwamnati mai shigar da kara ya bukaci karin lokaci don shiryawa a daidai lokacin da aka shirya kotun za ta saurari daukaka kara kan hukumci da wata karamar kotu ta yanke da ta hana belin tsohon ministan har zuwa ranar 8 ga watan Disamban inda za a fara shari'ar.
Sojojin kasar Zimbabwen sun kama tsohon ministan kudin Ignatius Chombo din ne da kuma tsare shi a daidai lokacin da suka shirya kwace mulki daga hannun tsohon shugaban kasar Robert Mugabe a kwanakin baya, kuma tun wannan lokacin ake tsare shi bisa zargin cin-hanci da rashawa da kuma yunkurin damfarar babban bankin kasar wasu makudan kudade a shekara ta 2004.
Mr. Chombo dai yana daga cikin 'yan siyasan da ake kira da G40 wadanda suke kurkusa da tsohon shugaba Mugabe da matarsa Grace wadanda kuma aka kora daga jam'iyyar ZANU-PF mai mulki din.