Kungiyoyi Sun Dakatar Da Ayukan Agaji A Afrika Ta Tsakiya
Bayanai daga Jamhuriyar Afrika ta tsakiya na cewa wasu kungiyoyin agaji sun yanke shawara dakatar da aikinsu, biyo bayan kisan wani jami'i a ranar Alhamis data gabata a wannan kasa.
KOda yake labarin bai mabato sunayen kungiyoyin ba, amma ya ce sun dau wannan matakin ne saboda yawaitar kai hare-hare wa tawaga da kuma sansanonin agaji a kasar, lamarin da ke kaiwa ga hasarar rayuka da kuma dukiyoyi.
Wata sanarwa da ofishin kula da ayukan jin kai na MDD cewa da (OCHA) a Afrika ta tsakiya ya fitar ta ce, tun daga farkon wannan shekara 2017, ma'aikatan jin kai 14 ne suka rasa rayukansu a Jamhuriya Afrika ta tsakiya.
Sanarwar wacce take nadamar hakan, ta ce a lardin Kabo dake gundumar Uham a arewacin kasar, kungiyoyin agaji da dama sun rufe kofofinsu saboda barazar da suke fuskanta.
A cewar ofishin na (OCHA) janyewar wadanan kungiyoyi a yankin zai jefa rayuwar sama da mutane dubu dari cikin halin ni 'yasu.