Rikicin Kasar Somaliya Ya Lashe Rayukan Duban Mutane
Cikin wata sanarwa da MDD ta fitar, daga watan Janairun 2016 zuwa watan Oktoban 2017, duban 'yan kasar Somaliya ne suka rasa rayukansu sanadiyar rikicin dake faruwa a cikin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto ofishin kare hakin bil-adama da ma'aikan agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Somaliya cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar a wannan Lahadi, sun sanar da cewa daga watan Janirun 2016 zuwa ranar 14 ga watan Oktoban 2017, akalla mutane dubu biyu da 78 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu dubu biyu da 507 suka jikkata sanadiyar rikicin dake faruwa a kasar.
Rahoton ya ce kashi 60% na wadanda hadarin ya ritsa da su, sanadiyar hare-haren ta'addancin kungiyar Ashabab ne.
A bangare guda, wata majiyar kasar ta Somaliya ta sanar da hallakar wani adadi na mayakan ashabab a yankunan kudu maso yammacin kasar a yayin wani gumurzu tsakaninsu da dakarun tsaron kasar.
Somaliya dai na daga cikin kasashen duniya dake fama da matsalar rashin tsaro a cikin goman shekarun baya-bayan nan.