Ana Fama Da Matasalar Karancin Man Fetur A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26257-ana_fama_da_matasalar_karancin_man_fetur_a_najeriya
Duk tare da umurnin gwamnatin tarayyar Nigeria ga ministan man fetur na kasar a ranar Laraba na ya gaggauta kawo karshen karancin man fetur a kasar hakan bai tabbata ba har jiya Litinin.
(last modified 2018-08-22T07:01:07+00:00 )
Dec 12, 2017 02:56 UTC
  • Ana Fama Da Matasalar Karancin Man Fetur A Najeriya

Duk tare da umurnin gwamnatin tarayyar Nigeria ga ministan man fetur na kasar a ranar Laraba na ya gaggauta kawo karshen karancin man fetur a kasar hakan bai tabbata ba har jiya Litinin.

Jaridar Premiumtimes ta Nigeria ta bayyana cewa a binciken da ta gudanar a jiya litinin ta gano cewa har yanzun akwai layukan ababen hawa a mafi yawan gidajen mai a birnin Abuja da sauran birnen kasar.

A ranar Laraba da ta gabata ce ministan watsa labarai Lai mohammad ya fadawa yan jarida, bayan taron majalisar ministocin kasar kan cewa za'a kawo karshen karancin man fetur a fadir kasar a cikin karshen mako mai zuwa.

Har'ila yau kamfanin man fetur na kasar NNPC, ta bakin kakakin kamfanin Ndu Ughamadu, ya fadawa yan jaridu a ranar Laraba kan cewa zasu kawo karshen layukan ababen hawa a gidajen man fitu a Abuja da sauran biranen kasar cikin sa'o'i. 

Premiumtimes ta tabbatar da cewa har ya zuwa jiya Litinin karancin mai sai dada karuwa yake sannan masu saida man a jarka-jarka sun sake bayyana a kan titunan biranen kasar.