Somaliya: Harin Kunar Bakin Waje Ya Kashe Mutane Uku A Birnin Magadishu
(last modified Thu, 14 Dec 2017 06:23:08 GMT )
Dec 14, 2017 06:23 UTC
  • Somaliya: Harin Kunar Bakin Waje Ya Kashe Mutane Uku A Birnin Magadishu

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto majiyar tsaro na cewa; Dan Kunar bakin waken ya sanya kakin 'yan sanda ne a lokacin da ya kai hari a sansanin bada horo na 'yan sandan kasar.

Kawo ya zuwa yanzu dai an tabbatar da mutuwar 'yan sanda uku da kuma maharin.

Wani jami'in 'yan sandan kasar ta Somaliya,  Muhammad Husain ya shaidawa kamfanin dillancin labarun reuters cewa; Kawo ya zuwa yanzu za mu iya tabbatar da mutuwar  mutane uku, amma abu ne mai yiyuwa adadin ya karu."

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai hare-hare irin wadannan ana danganta su da kungiyar al-shabab.