Sudan Ta Kudu: An Kafa Dokar Ta Baci A Jahohi Uku
Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Silva Kiir ne ya sanar da kafa dokar ta baci a jahohi ukun domin kwance damarar yaki a cikinsu.
Jahohin da dokar ta bacin ta shafa sune; Quk, Bahrul,Sharqi, da Bahrul Garbi. An kuma kira yi mazauna wadannan yankunan da su mika makamansu ga sojoji, idan kuma ba haka ba za su fuskanci doka.
Wan dan majalisar da ke wakiltar daya daga cikin yankuna da aka kafa dokar ta bacin, Darvi Mabor, ya sanar da cewa; a cikin mako guda daya da ya shude, fadan kabilanci a yankin ya ci rayukan mutane 170 da kuma jikkata wasu 200.
Kasar Sudan ta kudu tana fama da yaki a tsakanin sojojin da suke goyon bayan shugaban kasa da kuma masu goyon bayan mataimakinsa, tun a 2013. Bugu da kari kasar na fama da fadan kabilanci a yankunan daban-daban.