Madatsar Ruwa Ta Shalatin Zata Tada sabon Rikici Tsakanin Sudan Da Masar
Bayan da gwamnatin kasar Masar ta yanke shawarar gina madatsan ruwa a yankin Khaudai da Shalatin kan kogin Nilu, wata sabuwar rikici ta kunnu kanta tsakanin kasashen Sudan da Masar.
Wata jaridar kasar Qatar mai suna "Al-Jadeed" ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Sudan Ibrahim Ghandood yana cewa yerjejeniyar da Sudan ta cimma da Masar a kasar Saudia a baya, kan yan yanki mai kusuruwowi ukku na Shalatin bai yi mata da di ba, amma duk da haka a halin yanzu gwamnatin Masar tan shirin gina madatsan ruwa a yankin.
Tun bayan samun "yencin kan Sudan a shekara ta 1956 kasashen biyu suke takaddama kan mallakar yankin kan iyaka na kasashen biyu da ke kan Kogin Nilu wanda suke kira Hellibeen Triangle.
Kasar masar dai tana daukar yankin Shalatin mai yawan ruwan da ya kai mita murabaai miliyon 7, mai kuma zurfin mita 12 , a matsayin bangare na kasar Masar.