Najeriya Zata Kashe Dalar Amurka Bilyan Guda Don Yakar Boko Haram
Gwamnatin tarayyar Nigeria zata kashe dalar Amurka billion guda daga cikin kudaden raran man fetur kan shirinta na yaki da kungiyar boko haran a kasar
Jaridan Daily Trust ta Nigeria ta nakalto gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki yana fadar haka bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasar wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo. ya jagoranta a yau Alhamis.
Obaseki ya kara da cewa gwamnoni sun amincewa gwamnatin tarayyar ta fidda dalar Amurka billion guda don kammala yaki da ayyukan ta'addancin na Boko Haram.
Gwamnan ya ce a halin yanzu gwamnatin Nigeria tana da dalar Amurka billion 2.3 na kudaden rarar man fetur, don haka za'a kashe dala billion daya daga ciki don warware dimbin matsalolin da shirin yake da Boko haram ya ke fuskanta, wadanda suka hada da sayan makamai, da kuma kayakin aiki da ayyukan jami'an tsaro na farar hula.