An Fara Jigilar Bakin Haure Daga Kasar Libiya Zuwa Jamhuriyar Niger
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26397-an_fara_jigilar_bakin_haure_daga_kasar_libiya_zuwa_jamhuriyar_niger
Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da fara jigilar bakin haure daga kasar Libiya zuwa Jamhuriyar Niger da nufin maida su kasashensu na gado.
(last modified 2018-08-22T11:31:09+00:00 )
Dec 16, 2017 11:59 UTC
  • An Fara Jigilar Bakin Haure Daga Kasar Libiya Zuwa Jamhuriyar Niger

Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da fara jigilar bakin haure daga kasar Libiya zuwa Jamhuriyar Niger da nufin maida su kasashensu na gado.

A bayanin da Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a jiya Juma'a yana bayyana cewa: Bakin haure 74 ne kuma 51 daga cikinsu kananan yara 'yan asalin kasashen Eritrea da Somaliya aka fara jigilansu zuwa birnin Niemey fadar mulkin Jamhuriyar Niger bayan fito da su daga gidan kurkuku a kasar Libiya.  

Hukumar Kolin ta 'Yan Gudun Hijira ta kara da cewa: Tuni an shirya yadda za a kyautata wa 'yan gudun hijirar a kasar ta Niger da nufin kwantar musu da hankula kafin fara jigilarsu zuwa kasarsu ta gado.