An Bude Taron ECOWAS Karo Na 52 A Najeriya
Shugabannin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, na gudanar da taronsu karo na 52 a Najeriya wanda ke mayar da hankali kan matsalolin da suka shafi tattalin arziki da tsaro da rikicin Siyasa.
A lokacin bude taron Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce kyakkyawar alakar makwabtaka na da muhimmaci ga tsaro da ci-gaban tattalin arziki don haka ya zama wajibi a mayar da hankali wajen yakar barazanar 'yan ta'adda a yammacin afirka.
Kazalika Shugaba Buhari ya tabo batun cinikin bayi a kasar Libya inda ya ke cewa, 'tallafawa matasa da samar da ayyukan yi zai taimaka wajen dakile kwararar bakin-haure da ke jefa rayuwarsu cikin hatsari a Libya.'
Shugabannin ECOWAS za kuma su yi nazari kan hanyoyin shawo kan rikicin siyasar Togo da Guinea Bissau, da kuma samar da sauye-sauye kan ayyukan Kungiyar tare kuma yiuwar kasancewar kasar Marocco cikin mambobin kungiyar.
Ministan harakokin wajen Marocco ya ce kasarsa za ta jira har zuwa watanni uku na farkon sabuwar shekara ta 2018, domin ganin matakin da kungiyar ECOWAS din za ta dauka a game da kasar sa.