Dec 18, 2017 14:30 UTC

Gwamnatocin kasashen Faransa da Masar sun jaddada bukatar kara karfafa dangantakar soje da kuma tsaro a tsakanin kasashen biyu.

Shugaban kasar Masar Abdulfatah sisi da kuma ministan tsaron kasar Faransa Florence Parli sun bayyana cewa kasashen biyu zasu karfafa dangantakar tsaro da soje a tsakaninsu a cikin lokaci kadan nan gaba. A cikin yan shekaru da suka gabata dai jami'an gwamnatin kasashen biyu sun yi ta kaiwa juna ziyarori don karfafa dangantakar tsaro a tsakaninsu. A cikin ziyarar da ministan harkokin tsaron Faransa Florence Parli yake yi a halin yanzu a birnin Alkahira, batun karfafa harkokin tsaro a tsakaninsu, wadanda suka hada da sayarwa kasar Masar makamai da kuma sharara fage na ziyarar shugaban kasar Faransa zuwa Masar nan gaba,

Michel CABIROL, wani masanin harkokin tsaron yankin gabas ta tsakiya ya bayyana cewa ziyarar da Ministan tsaron kasar Farasan yake yi a halin yanzu a kasar Masar, sharara fage ne na ziyarar shugaban Emmanuel Macron na kasar Faransa zuwa kasar ta Masar.

Daga shekara ta 2015 ya zuwa yanzu kasar Masar ta sayi jiragen yaki samfurin Rafel 24 , jiragen ruwan yaki na zami guda daya da kuma makaman linzami da dama har'ila yau daga kasar Faransa wadanda kimarsu ya kai Euro billion 1 da milliyon 200.

Wasu masanan sun bayyana cewa karin hare-haren da yan ta'adda suke kaiwa a wurare daban daban a kasar Masar wani shiri ne na trilastawa kasar sayan karin makamai daga hannun kasar Faransa. Sun kuma kara da cewa yan ta'adda aka kasar Masar suna son rikata kasar ta Masar wacce ita ce kasa mafi yawan mutane a yankin gabas ta tsakiya, ta yadda duk abinda ya shafeta yana iya shafar dukkan yankin.

Banda haka ita kuma kasar Masar tana son ganinn ta mallaki makaman da zasu iya mayar mata da matsayin kasa wacce tafi karfi a yankin, bayan da wasu kasashen larabawa sun sha gabanta a halin yanzu.

A wani bangare kuma gwamnatin kasar ta Faransa tu rufe idonta a kan zarge-zargen da akewa gwamnatin kasar Masar ta take hakkin bil'adama, musamman tun bayan da shugaban kasa mai ci Abdulfatah Sisi yayi juin mulkiwa Mohammad Mursi a cikin watan Yulin shekara ta 2013.

 

 

Tags