An Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutane 21 A Masar
(last modified Tue, 19 Dec 2017 19:00:10 GMT )
Dec 19, 2017 19:00 UTC
  • An Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutane 21 A Masar

Kotun hukunta manya laifuka ta kasar Masar ta yanke hukuncin kisa kan wasu mutane 21 da ake zargi su nada alaka da wata kungiya mai dauke da makamai ta Damietta.

Kafar watsa Labaran Alyaumul-Sabi'i ta habarta cewa kotun hukunta manyan laifuka ta birnin Alkahira ta gudanar da zamanta a wannan talata a cibiyar shugabanin 'yan sanda na Tare, sannan ta yanke hukuncin kisa kan wasu mutane 21 da ake zargi su nada alaka da wata kungiya mai dauke da makamai ta Damietta.

Sanarwa da kotun ta fitar, laifin wadannan mutane shi ne shiga kungiyar da ba ta kan doka, da kuma yunkurin ta'addanci a kan sojoji da 'yan sanda, tayar da yamutsi a cikin kasar, da kuma hana jami'an tsaro gudanar da ayyukansu, ana sa ran za a karanto hukuncin  da aka yanke kan wadannan mutane a zama na ranar 22 ga watan Favrayu na shekarar 2018 mai kamawa.

A cikin shekaru 4 da suka gabata, an yanke hukuncin kisa kan daidaikun mutane ko kan wani gungun jama'a da ake zargi da laifin shiga cikin kungiyoyin da ba sa kan doka a kasar ta Masar, musaman ma kungiyoyin da suke da alaka da kungiyar 'yan uwa musulmi.

Saidai yanke hukuncin kisa a kan wani gungun jama'a na fuskantar suka a ciki da wajen kasar ta Masar.