FIDH Ta Zargi Jami'an Tsaron Congo Da Hannu A kisan Jama'a
Dec 20, 2017 07:49 UTC
Hukumar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa (FIDH) ta zargi jami'an tsaro kasar Congo da wata kungiyar mayaka da shirya kisan gillar da aka yi a yankin Kasai.
Hukumar ta ce jami'an tsaron sun aikata wannan ta'asar ce ta hanyar wata kungiyar mayaka dake samun goyan bayan sojojin kasar, a tsakanin watan Maris zuwa Yuli
Rahoton dai ya danganta lamarin da cin zarafin bil adama.
Rikicin da ya barke a yankin na Kasai dai ya yi ajalin mutum sama da 3,300.
Tags