Najeriya: An Kashe 'Yan Kungiyar Bokoharam 20 A Gabar Tekun Chadi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26541-najeriya_an_kashe_'yan_kungiyar_bokoharam_20_a_gabar_tekun_chadi
Kamfanin dillancin labarun Xinhua ta kasar Sin, ya ambato majiyar sojan Najeriya na cewa; Baya ga kashe 'yan ta'addar 20 an kuma kame wasu 17.
(last modified 2018-08-22T07:01:10+00:00 )
Dec 20, 2017 15:32 UTC
  • Najeriya: An Kashe 'Yan Kungiyar Bokoharam 20 A Gabar Tekun Chadi

Kamfanin dillancin labarun Xinhua ta kasar Sin, ya ambato majiyar sojan Najeriya na cewa; Baya ga kashe 'yan ta'addar 20 an kuma kame wasu 17.

Majiyar sojan ta kuma ce; A cikin makwanni biyu da suka fara kai hare-haren na kakkabe yankin tekun Chadi daga 'yan bokon haram din, sun kuma kai wasu hare-haren da manyan bindigogi da kuma jiragen sama.

Majiyar ta kara da cewa wasu sojoji 6 sun jikkata a yayin kai harin.

Sojojin Najeriya dai suna bayyana samun galaba akan kungiyar ta bokoharam wacce ta zama babban kalubalen tsaro tun 2009.

Kawo ya zuwa yanzu dai dubban mutane suka kwanta dama sanadiyyar hare-haren ta'addancin da kungiyar ta rika kai wa a cikin kasar da kuma  kasashen makwabta.