Rundunar 'Yan Sandan Zimbabwe Ta Kame Wasu Karin Tsoffin Ministocin Kasar Biyu
Rundunar 'yan sandan Zimbabwe ta sanar da kame wasu karin tsoffin ministocin kasar biyu kan zargin yin sama da fadi da dukiyar kasa.
Majiyar rundunar 'yan sandan Zimbabwe a yau Asabar ta fitar da sanarwar cewa: 'Yan sandan kasar sun kame Joseph Made tsohon ministan harkar gona ta kasar da Jason Mashaya shi ma tsohon minista a kasar kan zargin yin sama da fadi da duniyar kasa, kuma bayan kammala gudanar da bincike kansu za a tasar keyarsu zuwa kotu domin fuskantar shari'a.
Ci gaba da kame tsoffin jami'an tsohuwar gwamnatin Robert Mugabe ya zo ne bisa alwashin da sabon shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya yi na yaki da barnata duniyar kasa da nufin farfado da harkar tattalin arzikin Zimbabwe da ta durkushe tsawon shekaru tare da jaddada aniyarsa ta janyo baki 'yan kasashen waje domin sanya hannun jari a kasar.
Mnangagwa ya karbi ragamar shugabancin Zimbabwe ne tun a ranar 24 ga watan Nuwamban wannan shekara ta 2017 bayan da sojojin kasar suka tilastawa Robert Mugabe dan shekaru 93 a duniya yin murabus daga kan shugabancin kasar.