An Dauki Kwararan Matakan Tsaro Don Bukukuwan Kirsimeti A Gobe
Matsaloli masu muhimmanci biyu ne suke kan gaba a bukukuwan kirsimetin bana a tarayyar Nigeria, batun tsaro da kuma karancin man fetur.
Jaridar daily Trust ta Nigeria ta bayyana cewa a banagren tsaro an kai jami'an tsaro a wuraren bauta da kuma wurare masu muhimmanci a duk fadin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Nigeria NAN ya nakalto babban Sufeton 'yan sanda Mr Ibrahim Idris yana cewa ya bada umurnin kai jami'an tsaro a dukkan wurare masu muhimmanci da kuma wuraren bauta don tabbatar da cewa an gudanar da bukukuwan kirsimeti cikin natsuwa da zaman lafiya.
Sai dai a bangaren karancin man fetur kuma har yanzun ana fama da wahala wajen samunsa a gidajen mai, matsalar da hukumomi suka dora a kan 'yan kasuwa.
A wani bangaren kuma shugaba Muhammadu Buhari a sakonsa na kirsimeti ga kiristocin kasar a jiya Asabar ya bayyana cewa, duk tare da matsalolin da ake fama da su a kasar, yana fatan kwanaki masu kyau suna gaba, don a halin yanzu suna aiki tukuru a dukkanin bangarorin rayuwa na mutanen kasar don ganin an fice daga halin da ake ciki.