Ziyarar Shugaban Kasar Faransa Zuwa Jumhuriyar Niger
A ranar Jumma'a 22 ga watan Disamban da muke ciki ne shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kai ziyarar ba zata zuwa jumhuriyar Niger, inda ya gana da sojojin kasar ta Faransa da ke can, ya kuma gana da shugaban kasar ta Niger.
Gwamnatin kasar Faransa dai tana da sojoji kimani dubu4 a yankin yammacin Afrika inda suka aikin tabbatar da zaman lafiya a kasashen yankin tun da dadewa. Mohammad bin Chambas jakadan Majalisar dinkin duniya na musamman a yammacin Afrika, dangane da tashe-tashen hankula a yankin Sahel ya kuma yammacin Afrika yana cewa "yankin ya dade yana fama da masu tsatsauran ra'ayin addinin wadanda suka dade suka salwantar da rayuka da kuma dukiyoyi a yankin, wanda ya jawo kauracewar miliyoyin mutane daga gidajensu a kasashen daban-daban na yankin. Sanadiyar haka ayyukan raya kasa da kuma noma sun tsaya cik a wasu yankuna saboda rashin cikekken tsaro.
Wannan halin ne ya tilastawa kasar Faransa shigo da sojojinta kimani 4000 zuwa kasashe daban daban na yankin. A jumhuriyar Niger kamfanin Areva na kasar Faransa ce take hakan karfen Uranium fiye da shekaru 50 da suka gabata, kuma kowa ya san cewa kasar Niger tana daga cikin kasashen da suka fi kowa mallakar wannan karfin. Kasar Faransa ta fi kowa samun riba da wannan karfin a kasar Niger. Banda haka kasar Niger tana da wasu ma'adinai a karkashin kasa wadanda suka hada da man fetur da kuma zinari. A halin yanzu wasu kasashen masu gasa da kasar ta Faransa a samun amfani a jumhuriyar kamar kasar China tuni ta fara zuba jarai a bangaren man fetur a kasar. Don haka wannan gasar ta sa dole ne kasar faransa ta kawo sojojinta a yankin don kare wadannan amfaninta.
Banda wannan gwamnatin kasar Faransa tana tallafawa wata sabuwar runduna ta G_5 mai mayakan 5000 wacce kasashen Sahel guda 5 na yankin suka kafa. Kasashen sun hada da Chadi, Niger, Mauritania, Mali da kuma Borkina Faso. Manufar kafa wannan rundunar ita ce yaki da kungiyoyin yan ta'adda a wannan yankin.
Banda haka gwamnatin kasar Farasna ta ce zata bude ofisoshi a biranen Njamaina na kasar Chadi da kuma Yemai na jumhuriyar Niger don tantance matasan yankin wadanda suke son zuwa kasashen Turai, Faransa ta yi haka ne don kawo karshen hijira zuwa kasashen Turai mai halakarwa wanda matasan kasashen suke yi.
Daga karshe muna iya cewa ziyarar shugaba Emmanuel Macron a wannan karon shi ne karfafa guiwar sojojin kasar da suke aikin tabbatar da zaman lafiya nesa da gida, musamma a lokacin bukukuwan kirsimeta.