Sudan Ta Saki Jagorancin Tsibirin Suakin Ga Turkiya
(last modified Tue, 26 Dec 2017 11:03:09 GMT )
Dec 26, 2017 11:03 UTC
  • Sudan Ta Saki Jagorancin Tsibirin Suakin Ga Turkiya

Gwamnatin Sudan za ta mika wa Turkiya ikon tafiyar da tsibirin Suakin

Yayin da yake gabatar da jawabinsa jiya Litinin a birnin Khartoum na kasar Sudan, Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayib Erdogan ya bayyana cewa hukumomin birnin Khartoum za su saki ragamar tafiyar da tsibirin Suakin na tekun Maliya dake gabashin kasar ga Turkiya, domin su sake raya shi, da kuma kula da shi na wani lokaci da ba a kayyade ba.

Erdugan ya ce Shugban Umar Al-bashir ya amince da bukatar kasar Turkiya na karbar Tsibirin Suakin domin jagorantar shi na wani lokaci da ba a kayyade ba.

A ranar Lahadin da ta gabata ce, shugaban kasar Turkiya Rajab Tayib Erdogan ya fara ziyara aiki na kwanaki hudu a wasu kasashen Afirka  inda ya fara yada zango a kasar Sudan, inda bayan ya kamala ziyarar zai wuce zuwa kasashen Tchadi da Tunusiya.