Sudan Ta Saki Jagorancin Tsibirin Suakin Ga Turkiya
Gwamnatin Sudan za ta mika wa Turkiya ikon tafiyar da tsibirin Suakin
Yayin da yake gabatar da jawabinsa jiya Litinin a birnin Khartoum na kasar Sudan, Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayib Erdogan ya bayyana cewa hukumomin birnin Khartoum za su saki ragamar tafiyar da tsibirin Suakin na tekun Maliya dake gabashin kasar ga Turkiya, domin su sake raya shi, da kuma kula da shi na wani lokaci da ba a kayyade ba.
Erdugan ya ce Shugban Umar Al-bashir ya amince da bukatar kasar Turkiya na karbar Tsibirin Suakin domin jagorantar shi na wani lokaci da ba a kayyade ba.
A ranar Lahadin da ta gabata ce, shugaban kasar Turkiya Rajab Tayib Erdogan ya fara ziyara aiki na kwanaki hudu a wasu kasashen Afirka inda ya fara yada zango a kasar Sudan, inda bayan ya kamala ziyarar zai wuce zuwa kasashen Tchadi da Tunusiya.