Ana Ci Gaba Kidayen Kuri'un Zaben Shugaban Kasar Liberiya Zagaye Na Biyu
Rahotanni daga kasar Liberiya sun bayyana cewa an fara kirga kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka gudanar a jiya Talata tsakanin mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai da tsohon zakaran wasan kwallon kafa na kasar George Weah.
Rahotannin sun ce tun a daren jiya Talata din ce aka fara kidayen kuri'un da aka kada din a zagaye na biyu na zaben da ake sa ran zai kawo karshen mulkin shugabar kasar uwargida Ellen Johnson-Sirleaf wacce za ta gama wa'adin mulkinta na shekaru 12.
A bisa doka dai hukumar zaben kasar tana da wa'adin makonni biyu ne na ta sanar da sakamakon zaben na karshe, to sai dai wasu majiyoyi sun jiyo wasu jami'an hukumar suna fadin cewa akwai yiyuwar ma a gama aikin kidayar da kuma sanar da sakamakon zaben cikin kwanaki hudu masu zuwa.
Kimanin mutane miliyan 2.2 ne suka cancanci kada kuri'arsu a yayin wannan zabe wanda dukkanin alamu suke nuni da cewa George Weah, dan shekaru 51 a duniya, wanda shi ne ya zo na farko a zagayen farko na zaben, shi ne zai lashe shi sakamakon irin goyon bayan da yake da shi daga wajen matasan kasar. Rahotanni dai sun ce an sami karancin fitowar mutane a zaben na jiya idan aka kwatanta shi da irin fitowar da suka yi a zagayen farko na zaben, watakila hakan yana da alaka da dage asalin lokacin zaben da aka yi sakamakon karar da 'yan adawa suka shigar.