Mutane 7 'Yan Kasar Congo Sun Rasa Rayukansu Akan Iyaka Da Uganda
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26791-mutane_7_'yan_kasar_congo_sun_rasa_rayukansu_akan_iyaka_da_uganda
Wata Majiyar kasar ta Demokradiyyar Congo ta ce soja daya ne ya rasa ransa da kuma yan kungiyar nan ta Mai-mai shida
(last modified 2018-08-22T11:31:12+00:00 )
Dec 28, 2017 18:58 UTC
  • Mutane 7 'Yan Kasar Congo Sun Rasa Rayukansu Akan Iyaka Da Uganda

Wata Majiyar kasar ta Demokradiyyar Congo ta ce soja daya ne ya rasa ransa da kuma yan kungiyar nan ta Mai-mai shida

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto mazauna garin Kasindi da suka ganewa idanunsu abinda ya faru suna cewa; An yi taho mu gama da fada a tsakanin sojojin gwmanati da kuma kungiyar Mai-mai.

Sojojin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun kuma ce sune ke iko da yankin da fadan ya faru.

Gabacin Kasar Demokradiyyar Congo yana a matsayin sansanin da kungiyoyin tawaye na cikin gida da waje suke, suke kuma kai hare-hare a cikin kasar ta Dongo