An Kashe 'Yan Kaso 4 Yayin Da Suke Kokarin Gudu A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26801-an_kashe_'yan_kaso_4_yayin_da_suke_kokarin_gudu_a_najeriya
Kokarin jami'an tsaron Najeriya na hana 'yan kaso gudu daga gidan kason Akwa Ibom dake kudu maso gabashin kasar ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4.
(last modified 2018-08-22T07:01:12+00:00 )
Dec 29, 2017 03:03 UTC
  • An Kashe 'Yan Kaso 4 Yayin Da Suke Kokarin Gudu A Najeriya

Kokarin jami'an tsaron Najeriya na hana 'yan kaso gudu daga gidan kason Akwa Ibom dake kudu maso gabashin kasar ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto jami'an 'yan sandar garin Akwa Ibom na cewa wasu 'yan gidan kaso dake jihar sun far wa ma'aikatan dafa abinci , tare da karya kofa da kuma far wa jami'an tsaron gidan yarin.

Rahoton ya ce a karshen lamarin an bindige 'yan kaso hudu, sannan kuma an kame wasu guda bakwai yayin da suke kokarin,gudu, baya ga haka, jami'an 'yan sanda sun ce suna neman 'yan kaso 36 da suka gudu daga gidan yarin.

Duk da cewa jami'an 'yan sandar ba su bayyana dalilin da ya sanya 'yan kason na jihar Akwa Ibom tada wannan hatsaniya ba, to saidai ana kyautata zaton cewa  cunkoso da kuma rashin ingancin rayuwa a gidan kason shi ne ya haddasa wannan lamari.