An Kashe Jami'an Tsaron Masar 6 A Yankin Sinai Ta Arewa
Kakakin Rundunar tsaron Masar ya sanar da cewa Sojoji 6 ne suka rasa rayukansu sanadiyar fashewar Bam a yankin Sinai ta arewa.
Wata majiyar tsaron kasar Masar ta nakalto mai mai magana da rundunar tsaron kasar na cewa wani Bam da 'yan ta'adda suka dasa ya tashi da wata motar Sojin kasar a yayin da suke sintiri a yankin Mushrif zuwa kauyen Bi'iril-Abd dake jihar Sinai ta arewa, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar sojoji 6 tare da jikkata wasu uku na daban, daga cikin wadanda suka rasun har da wani soja mai mikamin kanal.
A safiyar jiya Alkhamis ma 'yan ta'adda sun harba makami mai linzamai kan wata mota mai sulke ta sojin Masar a garin Al-arish dake tsakiyar tsibirin Sinai lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wani soja da farar hula.
Jihar Sinai ta arewa ta kasance wata maboyar kungiyoyin 'yan ta'adda da suka jima suna kaddamar da hare-hare a kan jami'an tsaro da al'ummar kasar Masar.