Gwamnatin Gambiya Ta Sanar Da Shirinta Na Komawa Kungiyar Commonwealth
Gwamnatin kasar Gambiya ta sanar da majalisar dokokin kasar aniyarta na komawa cikin kungiyar Commonwealth ta kasashe rainon Ingila bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya fitar da kasar Gambiyan daga cikin kungiyar.
Kafar watsa labaran Africanews ta bayyana cewar ministan harkokin wajen kasar Gambiyan Ousainou Darboe, ne ya sanar da 'yan majalisar matsayar gwamnatin ta su lamarin da ya sami karbuwa daga kusan dukkanin 'yan majalisar.
Ministan harkokin wajen na Gambiya ya kara da cewa abin bakin ciki ne yadda tsohuwar gwamnatin Yahya Jammeh ta dauki matsayar ficewa daga kungiyar ba tare da shawartar majalisar, al'umma ko ma wasu cibiyoyin gwamnati da suke amfana da kungiyar ta Commonwealth ba.
A baya dai gwamnatin shugaba Adamu Barrow din ta sanar da cewa a ranar 11 ga watan Disamban nan ta mika takardun neman sake dawowa cikin kungiyar ta Commonwealth. A shekara ta 2013 ne tsohon shugaba Jammeh ya cire kasar Gambiya daga cikin kungiyar ta Commonwealth yana mai bayyana kungiyar a matsayin wata wata 'cibiya ta sabon mulkin mallaka'.