Buhari: A Shekara Mai Zuwa Akwai Kyakkyawar Fatan Ci Gaba
Shugaban Muhammadu Buhari na Nigeria ya bayyana cewa gwamnatinsa zata kammala wasu manya manyan ayyuka masu muhimmanci a shekara mai kamawa.
Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto shugaban yana fadar haka ne ta bakin kakakinsa fadar shugaban kasa Mr Femi Adesina a yau Asabar .
Ya kuma kara da cewa duk tare da matsalolin da gwamnatin take fuskanta a bangarori daban daban akwai kyakkyawar fata na farfadowar tattalin arzikin kasar da kuma daidaita farashin naira
A bangaren samar da wutar lantarki gwamnatin shugaba Buhari ta kashe naira billiyon 701 don tallafawa kamfanonin samar da wutar lantarki a kasar domin kyautata ayyukansu. Sannan ya ce a halin yanzu kasar tana samar da kimanin Megawatts 4000.
Mr Femi Adesina ya ce a cikin wannan shekara ne gwamnati ta fara biyan Penshon na yansandan Biyafara wadanda aka yi wa afuwa kimanin shekaru 17 da suka gabata.