Sojojin Masar Sun Kashe Kwamandojin Mayakan Yan Ta'adda 3 A Yankin Jiza
Ma'aikatar cikin gida na kasar Masar ta bada sanarwan cewa sojojin kasar sun sami nasarar kashe shuwagabannin kungiyoyin yan ta'adda a yankin Jiza na arewacin kasar sun kuma kama wasu 10.
Kafanin dillancin labaran Farsnews ya nakalto ma'aikatar tana fadar haka a yammacin yau Asabar, ta kuma kara da cewa yan ta'addan yayan kungiyar Hasm ne kuma an kashesu ne a maboyarsu da ke Al-qaliyubia da kuma Al-fayyum.
A ranar jumma'a da ta gabata ce wasu yan ta'adda suka kai hari kan cocin kiristocin kasar a kudancin birnin Alkahira suka kuma kashe mutane 10 daga cikinsu. Kungiyar yan ta'adda ta Daesh ce ta dauki nauyin kai hari na ranar Jumma'a . Banda haka a ranar Alhamis da ta gabata ma yan ta'adda a yankin Sina sun kashe jami'an tsaro 7 .