Tashin Bam Ya Hallaka Mutane 2 A Somaliya
(last modified Sun, 31 Dec 2017 19:18:48 GMT )
Dec 31, 2017 19:18 UTC
  • Tashin Bam Ya Hallaka Mutane 2 A Somaliya

Harin ta'addanci ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu da dama na daban a Magadushu babban birnin kasar Somaliya.

Jaridar Alkudusul-Arabie ta habarta cewa a ranar Assabar wani Bam ya tashi a kan hanyar tawagar Sojoji da ta kumshi dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen Afirka a Magadushu babban birnin kasar Somaliya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu, tare da jikkata wani adadi mai yawa, daga cikin wadanda suka hallakar har da jami'in tsaro guda.

Ya zuwa yanazu babu wani mutum guda da jami'an tsaron kasar ta Somaliya suka kama game da wannan hari na ta'addanci.

To saidai tuni kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab ta dauki nauyin kai harin, tare da riyar cewa sojoji biyu ne suka rasa rayukansu sanadiyar tashin bam din.

Kimanin shekaru 30 kenan da kasar Somaliyar ke fuskantar matsalar tsaro, inda a cikin shekarun baya-bayan nan kasar ke fuskantar hare-haren ta'addanci na kungiyar Ashabab, a halin da ake ciki, gwamnati na  jagorantar kasar ne bisa goyon bayan da dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen Afirka ke bata.