Ministan Harkokin Wajen Zambiya Ya Sanar Da Murabus Dinsa Daga Mukamin
(last modified Thu, 04 Jan 2018 05:49:02 GMT )
Jan 04, 2018 05:49 UTC
  • Ministan Harkokin Wajen Zambiya Ya Sanar Da Murabus Dinsa Daga Mukamin

Ministan harkokin wajen kasar Zambiya, Henry Kalaba, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa sakamakon gagarumin sabanin da ya kunno kai cikin jam'iyya mai mulki ta kasar kan batun tazarcen da shugaban kasar yake son yi.

Kafafen watsa labarai sun bayyana cewar ministan harkokin wajen na Zambiya ya sanar da murabus din nasa ne cikin wata sanarwa da ya watsa a shafinsa na Facebook inda ya ce aiki a irin wannan yanayi da rashawa da cin hanci suka zama ruwan dare, ba abu ne mai yiyuwa ba. Ministan ya kara da cewa mutanen da ya kamata su yi fada da rashawa da cin hancin su ne kan gaba wajen aikata shi, don haka ya zama wajibi yayi murabus daga mukamin nasa.

A baya-bayan nan dai an sami barkewar rikici tsakanin 'ya'yan jam'iyyar Patriotic Front (PF) mai mulki sakamakon aniyar shugaba Edgar Lungu na sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na uku, sabanin kundin tsarin mulkin kasar da ya kayyade wa'adin shugabancin kasar zuwa biyu da kowane shugaba.

Mr. Kalaba din dai, wanda dan majalisa ne daga jam'iyyar PF din yana daga cikin mutanen da ake ganin za su iya tsayawa takarar shugabancin kasar Zambiyan idan har shugaba Lungu ya sauka a karshen wa'adin mulkinsa na biyu a shekara ta 2021. Shi dai shugaba Lungu ya ce yana da hakkin sake tsayawa takarar don kuwa wa'adinsa na farko da yayi karashi ne na wa'adin mulkin shugaban kasar Michael Sata da ya mutu a kan karagar mulki.