Babu Hanyar Warware Matsalolin Yankin Gabas Ta Tsakiya In Banda Sasantawa
Ministan harkokin wajen kasar masar ya bayyana cewa babu wata hanyar warware rikice-rikicen kasashen Siriya da Libya in banda sulhuntawa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Sami Shukry ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a lokacinda yana ganawa tare da yan jarida a gaban tokoransa na kasar Jamus Heiko Maas a jiya Laraba.
Shukry ya kara da cewa gwamnatin kasar Masar a shirye take ta bada gudummawa don warware rikice rikicen kasashen Siriya da Libya cikin ruwan shniya da kuma tattaunawa. Ya ce dole ne a farfado da tattaunawar Geneva karkashin jagorancin Estefan Demestora jakadan majalisar dinkin duniya a kasar Siriya don kawo karshen rikicin kasar Siriya ta hanyar tattaunawa, hakama a rikicin kasar Libya inji shi.
Tun shekara ta 2011 da ta gabata ce, yan tawaye masu samun goyon bayan Amurka da kasashen Saudiya da kawayensu suka fara yunkurin kifar da gwamnatin kasar Siriya amma sun kasa kaiwa ga nasara haryanzun ba.