Najeriya: An Kama Wadanda Suka yi Kisa A Jihar Benue
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26993-najeriya_an_kama_wadanda_suka_yi_kisa_a_jihar_benue
Jami'an tsaro a jihar Benue da ke tarayyar Nigeria sun bada sanarwan kama mutane 8 daga cikin wadanda suka kashe mutane a jihar a bay bayan nan.
(last modified 2018-08-22T07:01:14+00:00 )
Jan 04, 2018 08:39 UTC
  • Najeriya: An Kama Wadanda Suka yi Kisa A Jihar Benue

Jami'an tsaro a jihar Benue da ke tarayyar Nigeria sun bada sanarwan kama mutane 8 daga cikin wadanda suka kashe mutane a jihar a bay bayan nan.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya bayyana cewa jami'an tsaron sun bada labarin kama mutane 8 bayan rikicin kabilancin tsakanin Fulani makiya da tibi a jihar. 

Majiyar yansanda a birnin Makurdi ta bayyana cewa an kama mutanen 4 a kananan hukumomi na Guma da Logo. Tun daga sanyin safiyar jiya Laraba ne matasa yan kabilar Tibi kimanin 3000 suka rufe wani babban titi a tsakiyar Makurdi inda suke neman gwamnatin tarayyar ta yi wani abu kan kisan da makon jiya wanda ya rutsa da yan kabilar su akalla 50.

Rikici tsakanin Fulani da makiya da kuma manoma yan kabilar Tibi ya lakume rayuka kimanin 300 a cikin shekaru biyu da suka gabata a jihar ta Benue.