Firaministan Somaliya Ya Yi Wa Gwamnatinsa Garan Bawul.
Firaministan kasar Somaliya ya gudanar da wasu canje-canje a gwamnatinsa inda ya sauki ministocin harakokin wajen da na kasuwanci.
Jaridar Alyaumu-sabi'i ya nakalto ministan sadarwar kasar Somaliya Abdurrahamane Usman Yarisou a wannan Alhamis na cewa Firaministan kasar Hassan Ali Khayre ya gudanar da wasu sauye-sauye a cikin gwamnatinsa a matsayin shirinsa na zartar da shirin gwamnati na kawo sauyi a kasar, wannan dai shi ne canji na farko da firaministan kasar ya yi tun bayan da ya samu wannan matsayi a watan Maris din 2017.
Guguwar sauyi ta yi da ministoci guda uku da suka hada da ministan harakokin wajen kasar da ministan kasuwanci gami da ministan cikin gida.
Wannan sauyi na zuwa ne a yayin da gwamnati ke fuskantar suka na kasar zartar da shirin da ta sanya a gaba na karya lagon kungiyar 'yan ta'adda ta Ashabab.
A shekarar da ta gabata,Mohamed Abdullahi Mohamed shugaban kasar ta Somaliya ya sauke ministan tsaron kasar bayan wani harin ta'addanci da mayakan Ashabab din suka kai a cikin Oktoban da ya gabata wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 512.
Kimanin shekaru 30 kenan da kasar Somaliya ke fama da matsalar rashin tsaro,wanda yanzu haka kasar ke samun taimakon rundunar wanzar da zaman lafiya na kasashen Afirka.