Sudan Ta Aike Da Dubban Sojoji Zuwa Kan Iyakokinta Da Eritrea
Rundunar Sojin Sudan ta aike da duban sojoji zuwa yankunan dake kan iyakokin kasar da kasar Eritrea.
Kafafen yada labaran kasashen larabawa sun habarta cewa wasu gungun 'yan tawayen yankin Darfur sun taru a yankunan dake kan iyakokin kasashen Sudan da Eritrea, kuma Masar ta aike da kayan yaki da suka hada da makamai, motocin soja masu sulke da kuma wasu na'urorin aikin soja zuwa sansanin sojin Sawa dake kasar Eritrea.
Shi dai wannan sansani na Sawa na wani yanki ne dake kusa da yankunan iyakokin kasar da gabashin kasar Sudan kuma shi ne babban sansani da ake horar da sojojin kasar ta Eritrea.
Kafafen yada labaran kasar Sudan sun nakalto Abdullahi Sadik Shugaban kwamitin iyakokin kasar ta Sudan na cewa kasar Masar na kokarin sanya kasar cikin rikici kai tsaye, baya ga sabani a kan rikicin gina madatsar ruwa da kasar Habasha take ginawa, kasashen biyu na da sabani kan wani yanki dake kan iyakokin kasashen biyu, inda kasar Sudan din ke ganin yankin mallakinta ne, Masar din ta mamaye.
A halin da ake ciki kasar Sudan din ta kira jakadanta dake birnin Alkahira.