Sama da mayakan Ashabab 20 ne aka hallaka a kasar Kenya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2707-sama_da_mayakan_ashabab_20_ne_aka_hallaka_a_kasar_kenya
Dakarun tsaron Kenya sun sanar da hallaka mayakan Ashabab a kudancin kasar Somaliya
(last modified 2018-08-22T11:28:00+00:00 )
Mar 20, 2016 15:14 UTC
  • Sama da mayakan Ashabab 20 ne aka hallaka a kasar Kenya

Dakarun tsaron Kenya sun sanar da hallaka mayakan Ashabab a kudancin kasar Somaliya

A wata sanarwa da ya fitar yau Kakakin Sojin kasar Kenya David Ubuntu ya ce Sojojin kasar sun samu nasarar hallaka mayakan Ashabab 21 a wani gumurzu da ya auku tsakanin Dakarun tsaron kasar da mayakan na Ashabab a kudancin Somaliya.

Ubuntu ya ce mutum biyu sun mutu daga cikin sojojin kasar yayin da wasu 5 na daban suka jikkata a yayin gumurzun, kuma lamarin ya auku ne a kusa da yankin Afkadu mai nisan kilomita 50 daga gabashin iyakar kasar da kenya.

A ranar Larabar da ta gabata ma mayakan na Ashabab sun yi kokarin kutsawa barikin Sojin Kenya dake yankin na Afkado, sai dai ba su samu nasara ba, inda aka yi ta masayar wuta a tsakaninsu, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka mayakan na Ashabab 19 inji majiyar tsaron ta kenya.

Duk da cewa Dakarun tsaron kasashen Afirka sun samu nasarar fatattakar mayakan Ashabab din daga wasu muhiman gariruwan Somaliya, saidai har yanzu, kasar na fuskantar hare-haren mayakan na Ashabab.