Mayakan Boko Haram 1050 Sun Mika Kansu Ga Sojojin Nijeriya
Majiyar sojojin Najeriya a yau Asabar ta bayyana cewa mayakan boko haram 1050 ne suka yi mika kansu ga sojojin kasar sannan wasu da sama sun ranta na kare a cikin yankin tapkin chadi da kuma garin Monguno a jihar Borno Borno.
Jaridar Daily Trust ta Nijerya ta nakalto Kanar Onyema Nwachukwu mataimakin daraktan shirin Operation Lafiya Dole ta samar da zaman lafiya a yankin yana fadar haka a yau a birnin Maiduguri.
Nwachukwu ya ce mayakan boko haram 250 daga reshen Al-Barnawi ne suka mika kansu ga sojojin Nijerya bayan barin wutan da aka yi masu a yankin tabkin Chadi. Sannan ya kara da cewa wasu mayakan 700 sun mika kansu ne ga sojojin Nijeria a garin Monguno.
Banda haka Nwachukwu ya ce wani babban komandan mayakan na boko haran Mamman Nura ya ji mummunan rauni sannan an kashe daya daga cikin matansa a wani harin da sojojin suka kai masu. Daga karshe ya ce wasu daga cikin wadanda suka arce sun mika kansu ga sojojin jumhuriyar Niger a yayinsa wasu kuma suna kokarin sajewa a cikin mutane a Kano, Gaidam, Hadeja, Gashuwa da kuma arewacin jihar Jagawa. Don haka ya bukaci mutanen wadannan yankuna su kula da sabbin fuskoki da suke shiga cikinsu.