Kasar Guinea Ta Maida Huldan Jakadanci Tare Da Kasar Italia
Kasashen Guinea Conakry da kasar Italia sun maida huldan jakadanci a tsakaninsu bayan katsewa na kimanin shekaru 10.
Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya bada labarin cewa a jiya jumma'a ne ministan harkokin wajen kasar Italia Angelino Alfano tare da tawagarsa suka gana da shugaban Alfa Conde inda kasashen biyu suka kuduri anniyar maida huldan jakadanci a tsakaninsu da kuma karfafa dangantakar kasashen biyu a bangarori daban-daban.
Har'ila yau labarin ya kara da cewa ministan harkokin wajen kasar ta Guinea Mamadi taraore ya gana da tokoransa na kasar ta Italia inda suka tattauna batun sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a babban biranen su.
A ranar 5 ga watan mayun shekara ta 2009 Mussa Dadis Camara wanda ya jagoranci wani juyin mulki wanda ba'a zubar da jima ba, bayan mutuwar shugaba Lansana Conte a rnar 22 ga watan Dusamba na shekara ta 2008, ya bada sanarwan katse huldan jakadanci da kasashen duniya da dama wadanda suka hada da kasar ta Itala. Camara bau bada dalilin daukar wannan matakin ba.