Sudan Ta Rufe Kan Iyakarta Da Kasar Eritrea
Rufe kan iyakar da Eritrea ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Khartum ta kafa dokar ta baci a jahar Kassala da ke kan iyaka.
gwamnan jahar ta Kassala Adam Jema ya bada umarni da dakatar da zirga-zirga akan dukkanin hanyoyin da ke isa kasar Eritrea, bisa dogaro da umarnin shugaban kasar Umar Hassan al-Bashir na kafa dokar ta baci.
Gwamnan jahar ta Kassala ya kuma ce; Sojoji sun isa cikin jahar ne domin karbe makamai daga hannun mutane da kuma fada da masu fasakwaurin mutane da kayan masarufi.
A gefe daya, wasu kafafen watsa labaru sun ambaci cewa Masar ta aike da sojojinta zuwa kasar Eritrea a wani abu da yake nuni da kamarin alaka da Sudan.
Alaka a tsakanin Masar da Sudan ta yi kamari saboda sabanin da suke da shi akan hakkin mallakar tsibiran Halayib, da a yanzu yake karkashin ikon Masar. Tuni dai Sudan ta kira yi jakadanta daga kasar Masar domin yin shawara.