An cabke Shugaban 'yan tawayen Tchadi a kasar Sudan
Mar 20, 2016 13:51 UTC
'Yan tawayen Tchadi sun bayyana damuwarsu kan kame shugaban su da aka yi a kasar Sudan
Gidan radion kasa da kasa na kasar Faransa ya habarta cewa an kame shugaban 'yan tawayen Tchadi Daoud Ali Bouyeneou a yayin da yake jiya a wata Asibiti dake garin Nyala na yammacin kasar Sudan.
'Yan tawayen na Tchadi sun nuna fargabarsu na yiyuwar meka shugaban na su ga magabatan birnin Njamena fadar milkin kasar Tchadi.
Kakakin 'yan tawayen Youssouf Hamid da yanzu haka ke kasar Turai ya ja kunan magabatan Sudan da kadda su kuskure su meka shugaban 'yan tawayen ga magabatan kasar ta Tchadi.
Tags