Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Kashe-Kashen Binuwai
Sufeto Janar na 'yan Sandan Nijeriya Ibrahim Idris ya bayyana cewar rundunar tasa ta shirya wajen kawo karshen kashe kashen da ke faruwa a jihar Binuwai na kasar yana mai cewa zai kai ziyara wasu garuruwa da rikicin yayi tsanani don gane wa idanuwansa abin da ke faruwa bayan da gwamnan jihar yayi zargin a nan ne aka tara masu kai hare-haren.
Mr Ibrahim Idris, sufeto janar na 'yan sandan Nijeriya ya bayyana hakan ne a yau din nan a wata ganawa da yayi da manema labarai inda ya ce a kokarin da gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ke yi na kawo karshen zubar da jinin da ke faruwa a jihar Binuwai din, ya kuduri aniyar kai ziyara wasu kauyuka da suka hada da Tunga, Guma and Logo da rikicin yayi tsanani.
Sufeto Janar din ya ce zai kai ziyara din ne bayan zargin da gwamnan jihar Binuwai din Samuel Ortom yayi na cewa masu dauke da makamin da suke kai hare-hare a jihar suna nan ne an tara su kauyen Tunga da ke jihar Nasarawa, don haka ya ce zai je ya gane wa idanuwansa musamman bayan da mutanen kauyen suka musanta wannan zargin. Sufeto Janar din ya ce tuni ya tura rundunonin 'yan sandan don tabbatar da zaman lafiya a jihar ta Binuwai da cikin kwanakin nan ke fuskantar hare-haren kisan gilla da wasu suke zargin fulani makiyaya da kai hare-haren.
A kwanakin baya ne dai shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari ya umurci sufeto janar din da ya koma jihar Benue din don sanya ido kan wannan lamari da kuma kawo karshen kashe-kashen.