Wasu Gwamnonin Arewacin Najeriya Sun Bukaci Shugaba Buhari Ya Yi Ta Zarce
Wasu Daga Cikin Gwamnonin arewacin Najeriya sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa ya nakalto wasu gwamnonin bakwai na Jam'iyyar APC , na cewa mafi dacewa shi ne shugaba Buhari mai shekaru 75 da haifuwa , ya zarce zuwa zagaye na biyu don ci gaba da gyara kasar.
A yayin ganawarsu da shugaban kasar Muhammadu Buhari bayan idar da sallar Juma'a a fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja, dukkanin gwamnonin sun nuna goyon bayansu da kuma tabbatar da cewa za su yi dukkanin abin da ya dace na ganin shugaba Buhari ya zarce a zaben 2019.
Gwamnonin da suka nuna sha'awarsu na goyon bayan Shugaba Buhari, sun hada da na jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da na Kaduna Nasir El-rufa'i da Yahaya Bello na Kogi da Simon Lalong na Plateau da kuma Jubrilla Bindow na Adamawa da Ibrahim Geidam Yobe da Abubakar Bello na Niger, sannan kuma sun yi wata ganawar sirri ta musamman da shugaban inda bakinsu ya hadu kan damarar da za su daura domin tunkarar zaben na 2019.