Al-Azhar Ta Yi Suka Kan Zancen Trump Na Wulakanta Wasu Kasashe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27277-al_azhar_ta_yi_suka_kan_zancen_trump_na_wulakanta_wasu_kasashe
Jami'ar Al-Azhar ta kasar Masar ya yi Allah wadai da kalaman wulakanci da kaskanta wasu kasashen duniya wanda shugaban Amurka ya yi
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jan 14, 2018 15:29 UTC
  • Al-Azhar Ta Yi Suka Kan Zancen Trump Na Wulakanta Wasu Kasashe

Jami'ar Al-Azhar ta kasar Masar ya yi Allah wadai da kalaman wulakanci da kaskanta wasu kasashen duniya wanda shugaban Amurka ya yi

Jaridar Raayul-Yaum ta kasar ta Masar ta buga wani bayanin da jami'ar ta fitar a yau Lahadi, inda ya kara da cewa irin wadannan kalamai sun sabawa mutuntaka da kuma zama tare. Banda haka sun sabawa 'yncin bil'adama da kuma kare hakkinsa.

Daga karshe Jami'ar ta bukaci shugaban ya nemi afwa daga wadanda ya wulakanta da wadannan maganganunsa. 

A ranar Alhamis da ta gabata ce shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya sifanta wasu kasashen Afrika da kuma kasashen Haiti da Elsalvado a matsayin gidajin shara, ya kuma bukaci a dakatar da karban baki daga garesu.